• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GUDANAR DA JANA’IZAR BABBAN HAFSAN SOJAN KASAN NAJERIYA DA TAWAGAR SA

An gudanar da jana’izar marigayi babban hafsan sojan kasan Najeriya laftanar janar Ibrahim Attahiru wanda ya riga mu gidan gaskiya da ‘yan tawagar sa a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

An yi sallar marigayin a babban masallacin Abuja da kuma na mabiya addinin kirista a wata cibiyar kirista ta sojan sama a hanyar filin saukar jiragen sama na Abuja.

Dafifin jama’a da ‘yan uwan marigayan sun taru don nuna juyayin kan wannan rashi da ya shafi kasa gaba daya.

Rundunar soja ta yi karramawa ta musamman ga marigayan a makabartar soja da ke Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.