An gudanar da idin karamar sallah lami lafiya a sassan Najeriya inda malamai su ka gabatar da nasiha da jagorantar addu’ar samun zaman lafiya da tsaro a kasa.
Kama daga Sokoto har zuwa Maiduguri, daga Lagos har Yola an ga mutane na tururuwa zuwa masallatan idi don gudanar da sallah.
A Abuja an takaita yin sallar a masallatan jumma’a ne maimakon zuwa filin idi bisa dalilan da ba sa raba nasaba da tsaro.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya taya musulmi murnar idin, ya yi sallar a Abuja da yin murna cikin takaitattun mutane a fadar Aso Rock.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀