• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GARZAYA DA ABDULRASHID MAINA GIDAN YARI DON DAURIN SHEKARU 8

Bayan hukuncin alkalin babbar kotun taraiya a Abuja, an garzaya da tsohon shugaban kwamitin kudin fansho Abdulrashid Maina gidan yari don fara zaman daurin shekaru 8, duk da za a fara lissafi ne daga Oktoba ta 2019 lokacin da a ka fara gurfanar dabshi gaban kotu.

Alkalin babbar kotun Jostis Okon Abang ne ya yanke hukuncin bayan shari’ar da ta kai shekaru biyu a na gudanarwa kan laifin sama da fadi na naira biliyan 2.

Jostis Abang kazalika ya ce da ya dace a hada da bankunan da Maina ya yi amfani da su wajen kwashe kudin fanshon da su ka hada da UBA da Fedelity.

Kotun ta ce ya dace a ma janye lasisin bankunan biyu.

Hakanan kotun ta yi umurnin kamfanin Maina ya dawowa da gwamnatin taraiya naira biliyan daya zuwa nan da wata uku kuma ta yi umurnin kwace wata mota mai sulke da wasu gidaje a anguwar Jabi Abuja.

Kotun ta zaiyana Maina a matsayin wanda ba ya tausayin ‘yan fansho.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.