• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GA WATAN RAMADAN NA BANA A NAJERIYA DA NIJAR

ByNoblen

Apr 13, 2021

An ga watan ramadan na bana hijira 1442 a Najeriya kamar yanda mai alfarma sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar.

Don haka a talatar nan 13 ga watan nan na Afrilu za a fara azumin.

A Najeriya an ga watan yayin da watan sha’aban ya cika kwana 29.

Sultan Muhammad Sa’ad ya bukaci masu ibada su rika kula da yanayin annobar don kare kan su daga korona bairos musamman wajen itikafi.

Hakanan an ga watan a jamhuriyar Nijar a yankuan kasar da su ka hada da Agadez.

Tuni Saudiyya ta sanar da ganin watan yayin da lissafin watan sha’aban ya cika kwana 30.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *