• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN FARA JIGILAR ALHAZAN NAJERIYA ZUWA SAUDIYYA DAGA MAIDUGURI JIHAR BORNO

An kaddamar da jigilar alhazan Najeriya na bana daga filin jiragen sama na Maiduguri da ke jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Jirgin Max ya tashi da alhazai 529 kuma ya nufi birnin Madina ne.

Shugaban hukumar alhazan NAHCON Sheikh Zikrullah Kunle Hassan da kuma gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum.

Wannan ya nuna daga yanzu jiragen za su cigaba da tashi don isar da maniyatan Najeriya zuwa Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana bayan dakatar da alhazan ketare da Saudiyya ta yin a tsawon shekaru a sanadiyyar cutar annoba.

Kamfanonin jirage uku ne za su yi jigilar inda a cikin su akwai Flynas wanda na Saudiyya ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.