• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN FARA AIKIN HAJJIN BANA HIJRA 1442

Alhazai sun shiga Makkah ta mashigu hudu don yaki da cutar annoba inda su ka isa masallacin dakin Ka’aba su ka yi dawafi don shirin tafiya filin arfa a litinin din nan.

Alhazan dai dubu 60 daga iya cikin Saudiyya ba za su rasa haduwa da wasu kalilan daga jami’an gwamnatocin duniya da a ka ba wa damar zuwa hajjin ba.

Bayan kammala dawafin an shiga jigilar alhazan zuwa wasu gidaje da ke daf da wajajen aikin hajji wato inda ya hada da Muna, Muzdalifa da Arfa.

Da zarar kowane rukuni ta gama dawafi, a kan fesa magani a haramin don kara kula da lafiyar alhazai.
Da yawa masu amfana da zuwan alhazai daga ketare ko kuma masu shaukin ganin baki na cikin juyayi da zubar da hawaye kan yanda tamkar Makkah ke wayam a wannan lokaci na shekara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *