• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN DAWO DA AIKI DA SHIRIN SAKE TAFIYA HUTUN SABUWAR SHEKARAR MILADIYYA A NAJERIYA

An dawo aikin gwamnati a Najeriya ranar talata bayan hutun bukin kirsimeti na mabiya addinin kirista da ya kammala a ranar litinin.

Yanzu ma ma’aikata na shirin sake yin wani hutun ranar jumma’ar nan mai zuwa da ta zo daidai da daya ga watan janairun sabuwar shekarar miladiyya ta 2020.

Bitar shekara ta 2020 na nuna yawan juyayi na rasuwar mutane da dama a kusan kowanne sashe na Najeriya.

Hakanan a shekarar ce a ka sake samun tashin farashin man fetur a lokuta daban-daban har ta kai ga mutane sun daina damuwa da ragi ko karin farashin.

Kazalika a shekarar a ka samu mafi tsawon yajin aikin kungiyar malaman jami’a ASUU na wata tara cur.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.