• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN DAKATAR DA SHUGABAR HUKUMAR TASHOSHIN JIRAGEN RUWA HADIZA BALA DAGA MUKAMIN TA

Rahotanni na baiyana dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya Hadiza Bala Usman daga mukamin ta.

An fahimci cewa dakatarwar ba za ya rasa nasaba da bayanin rashin jituwa da ke tsakanin ta da ministan sufuri Rotimi Ameachi ba saboda yanayin miskilancin ta.

Shugaba Bubari ya nada Hadiza a farko  a 2016 kuma ya sake nada ta a watan Janairu na bana don cigaba da wa’adi na biyu.

Gabanin nadin ta, gwamna Nasiru Elrufai ya nada ta shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin sa inda gabanin nan kuma ta kasance cikin ‘yan gwagwarmayar ceto matan Chibok wato bringbackourgirls.

A na sa ran minista Amaechi ya baiyana dalilan dakatar da Hadiza a jumma’ar nan.

Hadiza Bala Usman ‘yar maraigayi Dr.Bala Usman na jami’ar Ahmadu Bello ta taya shugaba Buhari kamfen a 2015 inda a ke ganin ta a tawagar shugaban lokacin da ya ke takarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN DAKATAR DA SHUGABAR HUKUMAR TASHOSHIN JIRAGEN RUWA HADIZA BALA DAGA MUKAMIN TA”
  1. I absolutely love your website.. Pleasant colors & theme. Did you create this site yourself?
    Please reply back as I’m attempting to create my very own blog and would love to know where you got this from or just what the theme
    is named. Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published.