Wasu sun kai farmaki kan ofishin bangaren Ibrahim Shekaru na APC a Kano ta hanyar cinnawa ofishin wuta.
Ofishin dai na kamfen din Sanata Barau Jibrin, na kan titin Miaduguri a yankin Hotoro a jihar Kano.
Mutane dai sun yi maza-maza su ka taimaka wajen kashe wutar da kuma tunkarar wadanda su ka kawo farmakin.
In za a tuna babbar kotun taraiya a Abuja ta amince da bangaren karkashin jagorancin Haruna Danzago a matsayin sahihin jagorancin APC a jihar da rushe bangaren Abdullahi Abbas.
Jami’an tsaro sun garzayo wajen don tabbatar da doka da oda.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀