• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN CIGABA DA SAMUN RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA A SATUMBA KAI KA CE AGUSTA NE

ByNoblen

Sep 12, 2022

An cigaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan Najeriya a cikin watan satumba tamkar yanda a ka saba samu a watan agusta.

An share wuni biyu a Abuja a na samun ruwan inda hakan ya sa ya zama ko mutane su yi kunduma su fita a cikin ruwan ko su cigaba da fakewa a gida da sauran wajajen da ke da rumfuna.

A kan samu inda ruwan kan kwanta a kan titi a tsakiyar birnin don yawan sa ba wai don ba hanyoyin magudanan ruwa ba ne.

Hakika yankunan da ke makwabta da Abuja da ba su da wadatattun magudanan ruwa ko jama’a sun tose su da shara na fusknatar barazanar ambaliyar ruwa.

Masu sayar da lema da magogin gilashin mota na samun ciniki da yanayin ya tilasta sayan irin wadannan kaya don amfanin su ya zo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “AN CIGABA DA SAMUN RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA A SATUMBA KAI KA CE AGUSTA NE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.