• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

An cafke mutane 5 da suke kai ma ‘yan bindiga man fetur a Jihar Katsina.

ByAuwal Ahmad Shaago

Sep 22, 2021

Rundunar Yan’sadan jihar Katsina ta Samu Nasarar kama mutane biyar a jihar Katsina da laifin kaima ‘yan bindiga Man fetur.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, wanda ya bayyana wadanda ake zargin a ranar Talata 21/9/2021. A wata sanarwa da fitar, ya ce “an kama wani mutum mai shekaru 32 daga Maradi, Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar yana jigilar Man a cikin motar.

“Haka kuma an kama wani mutum mai shekaru 28, mazaunin Magamar Jibia, yana Safarar Man fetur a cikin motar sa ta mai kirar Passat.”Rundunar ta kuma samu nasarar cafke wani dattijo dan shekara 50, mazaunin kauyen Daddara, a karamar hukumar Jibia, wanda kuma ake zargin yana kawo Man fetur a cikin motarsa mai ​​kirar Golf III.

Sai kuma wani mutum mai shekaru 57, wanda shima ake zargi da safarar Mai a Unguwar Kofar Guga Quarters. Gambo Isah ya ce “wadanda ake zargin sun furta cewa sun sayar da Man a gefen dajin, sabanin umarnin gwamnati.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *