• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Biyo bayan kama tsohon shugaban kwamitin aiki da cikawa na fansho Abdulrashid Maina a Nijar, yanzu dai a na shirin dawo da shi Najeriya.

Kakakin ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya ce ‘yan sandan Najeriya da hadin guiwar na Nijar su ka cafke Maina a Yamai babban birnin Nijar.

Mba ya ce a na shirin dawo da Maina daga Nijar don ya cigaba da fuskantar shari’a.

Alkalin kotun taraiya ta Abuja Okon Abang ya aiyana neman Maina ruwa a jallo inda har ta kai ga adana wanda ya tsaya ma sa wajen beli Sanata Ali Ndume a gidan yari na wasu kwanaki. 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.