• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN BUDE GASAR KARATUN ALKUR’ANI MAI GIRMA DA GIDAN TALABIJIN DIN GASKIYA YA SHIRYA

An bude gasar karatun Alkur’ani mai girma da gidan talabijin na Gaskiya mai cibiya a Ghana ya shirya a babban birnin Najeriya Abuja.
Gasar wacce a ka fara daga matakin jihohi, ta shafi dukkan jihohin arewacin Najeriya 19 in ban da Kwara.
Jagoran gasar Dr.Abdulkadir Saleh Kazaure ya ce gasar ta yara da matasa maza da mata ‘yan kasa da shekara 20 da ke da haddar Alkru’ani.
Dr.Kazaure ya ce yayin da maza ke gasar izu 60 na Alkur’ani, mata na yin izu 30 ne kuma za a kammala a alhamis din nan.
Daya dsaga limaman masallacin taraiya na Abuja Dr.Muhammad Kabir Adam ya ce ya na da muhimmanci duk iyaye su tabbatar ‘ya’yan su, na koyon karatun Alkur’ani don samun haddace shit un su na da karancin shekaru.
Dr.Adam ya ce shagaltar da yara da karatun Alkur’ani zai saita al’umma ta zama da albarka da kuma zaman lafiya.
Za a raba manyan kyautuka wadanda su ka fi kwazo dala dubu 5 ga kowanne da kujerar Makkah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AN BUDE GASAR KARATUN ALKUR’ANI MAI GIRMA DA GIDAN TALABIJIN DIN GASKIYA YA SHIRYA”
  1. I’ll immediately snatch your rss feed as I can’t find your e-mail subscription link or e-newsletter service. Do you have any? Please let me realize so that I may just subscribe. Thanks.

Leave a Reply

Your email address will not be published.