• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN BANKAWA OFISHIN HUKUMAR ZABE WUTA A ESSIEN UDIM A AKWA IBOM

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce an bankawa ofishin ta da ke karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom wuta.

Kwamishinan labaru na hukumar Festus Okoye ya baiyana haka a wata sanarwa.

INEC ta ce mai gadin ofishin ya samu ya arce daga ofishin ba tare da samun rauni ba.

Kazalika sanarwar ta zaiyana cewa wasu ne da ba a san ko su waye ba su ka kai harin.

Motoci, akwatunan zabe da sauran takardu sun kone kurmus a ofishin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *