• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN BAIYANA TSARIN GUDANAR DA IBADA A RAMADAN

ByMardiya Musa Ahmed

Mar 25, 2022

An fito da tsari mai inganci don gudanar da ibada a watan ramadan mai tinkarowa a masallacin dakin Ka’aba da ke Makkah da masallacin Manzon Allah da ke Madina.
Shugaban kula da masallatan biyu Dr.Abdulrahman Sudai ya baiyana tsare-tsaren a wani taro da ya samu halartar mukaddashin ministan labaru Dr.Majid bin Abdullah Al-Qasabi.
Dr.Sudais ya ce duk da an sassauta matakan yaki da annobar korona, amma za a tabbatar an kula da lafiyar al’umma.
Saudiyya dai ta bude damar shiga kasar ta daga ketare bayan a can baya ta takaita shigar jama’a don samun nau’in annobar korona mai suna OMICRON.
Sabbin matakan na Saudiyya na ba da kwarin guiwar yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.