An ba wa hukumar binciken hatsari ta Najeriya “AIB” ta binciki musabbabin faduwar jirgin soja da ya yi sanadiyyar mutuwar babban hafsan sojan kasan Najeriya.
Tuni an samo bakin akwatin tattara bayanai na jirgin sojan.
Jami’in labarun hukumar Tunji Oketunbi ya ce za a gudanar da binciken da na’urorin jirgin da a ka dauko a dakin binciken su da ke Abuja.
Wata yarjejeniya tsakanin hukumar da a ka cimma a bara ta ba da damar gudanar da wannan bincike waje da rundunar soja.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀