• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA RUBUTA SUNAYEN JAMI’AN IRAN DA DAMA A BAKIN LITTAFI DON ZARGIN SU DA TAKE HAKKIN DAN ADAM

Amurka ta sanya takunkumi kan jami’an Iran da dama don zargin su da aiyuka daban-daban na take hakkin dan adam.

Jami’an sun hada har da alkalin kotun Shiraz wanda ya saurari shari’ar dan kokawar nan ta zamani Navid Afkari har a ka yanke ma sa hukuncin kisan.
Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya ce Amurka ta sanya sunan alkali Sayed Mahmoud Sadati a bakin littafi don hannun sa a shari’ar da ta kai ga zartar da hukuncin kisa ga Afkari.

Sauran mutanen da takunkumin ya shafa sun hada da Allaki Mohammad Soltani, gidan yarin Adel Abad, gidan yarin Vakilabad da sauran su.
Iran ta samu Afkari da laifin dabawa wani jami’in tsaro wuka a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta Iran a 2018 don korafin tsadar rayuwa, cin hanci da rashawa da mulkin kama-karya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AMURKA TA RUBUTA SUNAYEN JAMI’AN IRAN DA DAMA A BAKIN LITTAFI DON ZARGIN SU DA TAKE HAKKIN DAN ADAM”
  1. I’m really impressed with your writing skills and also with the
    layout on your blog. Is this a paid theme or did you customize it yourself?
    Either way keep up the excellent quality writing, it’s rare to see a nice blog like this one these days.

Leave a Reply

Your email address will not be published.