• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA NUNA KARSHE DAI ITA MA KASAR KATAR ZA TA KULLA DANGANTAKA DA YAHUDAWAN ISRA’ILA

Ma’aikatar wajen Amurka ta ce karshe dai ita ma kasar Katar za ta kulla dangantaka da Yahudun Isra’ila duk da yanda a yanzu ta yi watsi da dangantakar da Daular Larabarwa da Bahrain su ka kulla da Isra’ila a fadar White House mai taken SULHUN IBRAHIM ko “ABRAHAM ACCORDS” a turance.Mataimakin sakataren wajen Amurka mai kula da lamuran kasashen Larabawa Timothy Landerking, ya ce ai Katar ce ta farko da ta samar da fagen kafa ofishin jakadacin Isra’ila a birnin Doha. Landerking ya ce Katar ma na bayanai masu ma’ana in an kwatanta da Turkiyya da ta fito karara ta yi tir da dangantaka da Yahudawan. Katar dai ta sha kalubalantar Isra’ila inda kuma ta nuna ba za ta yi huldar da Isra’ila ba sai ta san matsayin Palasdinawa. Da alamu shugaban Amurka Donald Trump na kara dagewa wajen samawa Yahudawa karbuwa a wajen Larabawa don hakan ya zama karin karfi a gwamnatin sa gabanin babban zaben kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.