• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA MIKA FILIN SAUKAR JIRAGE NA BAGRAM GA GWAMNATIN AFGHANISTAN

Bayan kimanin shekaru 20, Amurka ta mika filin saukar jirage na Bagram ga gwamnatin Afghanistan.

Sojojin Amurka sun yi amfani da filin jirgin wajen yaki da ‘yan Taliban karkashin Mullah Omar da Osma Ben Laden.

Wannan na nuna Amurka na aikin kammala janye sojojin ta 2,500 – 3,500  daga Afghanistan don aiyana kammala wannan yaki da ya dade ba a kammala ba.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alwashin janye dukkan sojojin Amurka daga Afghanistan zuwa 11 ga watan satumba.

Yawancin sojojin taron dangi na kungiyar tsaro ta yamma “NATO” syn sulale daga Afghanistan ba tare da sanarwa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *