• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA KYAUTATA DIFLOMASIYYA DA SUDAN

ByNoblen

Jun 29, 2021 , ,

Amurka ta baiyana inganta harkokin diflomasiyyar ta da kasar Sudan da ke zaman doya da manja tun mulkin tsohon shugaban kasar Omar Elbashir.

Jami’in ofishin jakadancin Amurka a birnin Khartoum na Sudan Amber Baskett ya baiyana matsayar ta Amurka don nuna gwamnatin rikwan kwarya ta kasar ta samar da sauye-sauye masu ma’ana.

Ministar wajen Sudan Maryam Al-Sadiq ce ta marabci Baskett, ta na mai cewa matakin na Amurka zai taimakawa gwamnatin rikwan kwaryar wajen cimma nasarorin da ta sa a gaba na maida kasar hannun zababbiyar  gwamnatin dimokradiyya.

Tun kawar da gwamnatin Elbashir a 2019, Amurka ke matsowa don hulda da Sudan har ma da cire kasar daga jerin kasashen da Amurka ke zargi da daukar nauyin ta’addanci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *