• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA KWACE BINDIGOGI DA ALBARUSAI A WANI JIRGIN KAMUN KIFI NA IRAN

ByNoblen

Dec 24, 2021 , ,

Sojojin ruwan Amurka sun kwace bindigogi da labarusai a cikin wani jirgin kamun kifi na Iran da a ke ganin za a kai wa ‘yan tawayen Yaman ne da ke cigaba da mamaye babban birnin na Yaman wato San’a’a.
Amurka ta gano jirgin ne a binciken da sojojin na ta ke yi a gabar ruwan Pakistan da Oman tun ranar litinin.
Dakarun sun shiga jirgin su ka samu bindigogi samfurin AK 47 guda 1,500 da kuma albarusai 226,600.
Iran na nuna kin amincewa da cewa ita ke ba wa ‘yan tawayen houthi makamai, duk da hujjojin da a ke da sun a nuna makaman kirar Iran ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *