• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA TA KAKABA TAKUNKUMIN HANA VISA GA MASU MAGUDIN ZABE A NAJERIYA

A matakan da ta ke dauka na bunkasa turbar dimokradiyya a duniya, Amurka ta kakaba takunkumin ba da VISA ga wasu daga ‘yan siyasar Najeriya da su ke da hannu wajen magudi da sauran dabi’u da su ka kawo cikas a lokacin zaben gwamnan Kogi da Bayelsa. Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki gabanin zaben gwamnan jihar Edo a ranar asabar din nan 19 ga watan nan na satumba. Ma’aikatar wajen Amurka ta baiyana cewa Amurka na yabawa ‘yan Najeriya ga irin abun da su ka yi a babban zabe na 2019 amma a lokaci guda ta caccaki wadanda ke da hannu a magudin zabe. Sanarwar ta Amurka ba ta jera sunayen wadanda lamarin ya shafa ba amma dai za su iya fahimtar hakan musamman in sun nemi izinin shiga Amurka. Sanrawarta kara da cewa sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya kara daukar matakan sanya takunkumin ba da izinin shiga Amurka amma ga wasu ajin mutane masu zagon kasa ga dimokradiyya; inda hakan baya nufin sanya ‘yan Najeriya a gaba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AMURKA TA KAKABA TAKUNKUMIN HANA VISA GA MASU MAGUDIN ZABE A NAJERIYA”
  1. I’m curious to find out what blog platform you are working with?
    I’m having some minor security issues with my latest site and I’d like to find something more
    secure. Do you have any recommendations?

  2. When someone writes an post he/she maintains the thought of a user in his/her mind that how a user can know it.
    Thus that’s why this article is outstdanding. Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.