• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMURKA NA DAUKAR GWAMNATIN ABED RABBO A MATSAYIN JAGORAR YAMANAWA

Amurka na daukar zababbiyar gwamnatin Abed Rabbo a matsayin jagorar Yamanawa duk da su kuma ‘yan houthi na rike sassan kasar.

Ma’aikatar wajen Amurka ta baiyana haka ranar jumma’a.
Bayanin na zuwa ne kwana daya bayan jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya Tim Lenderking ya ce ya na daukar ‘yan tawayen houthi a matsayin halaltaccen karfi a Yaman.

Gwamnatin Yaman da Yamanawa da dama da ba sa danyen ganye da houthi sun ji haushin kalaman na Landerking da ke zaman tamkar Amurka ta sauya matsaya kan lamarin na houthi.

Wannan ne ya sa Amurka ta fito ta faiyace matsaya a kan tabbatar da hakkin mulki ga gwamnatin Abed Rabbo Mansour Hadi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *