• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMSA LAIFIN MUTUM BIYU CIKIN 7 YA SO KAWO GARDAMA A SHARI’AR ABBA KYARI

Amsa aikata laifin fataucin kwaya da biyu daga mutum 7 da a ke zargi a shari’ar DCP Abba Kyari ya kawo gardama a shari’ar da a ka fara.
Rundunar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta gurfanar da Abba kyari da ke cikin mutum 7 da ta ke tuhuma da fataucin miyagun kwayoyi.
Biyu daga wadanda a ke tuhuma da su ka hada da Chibuna Umeibe da Emeka Ezenwanne sun amince da ikata 3 cikin caji 8 da a ke yi mu su.
Lauyan NDLEA Joseph Sunday ya bukaci alkalin kotun ya fara shirin yankewa mutanen biyu hukunci tun da sun amsa laifin su.
Nan take lauyan Kyari wato babban lauya Kanu Agabi ya yi ki amincewa da batun yanke hukuncin, ya na mai cewa mutanen biyu sun amsa laifin ne bisa jahilci.
Agabi ya ce yanke hukuncin zai birkita lamuran shari’ar.
Alkalin kotun Mr.Nwite ya bukaci lauyoyin sassan biyu su daidaita bayanan su inda y adage sauraron karar zuwa 14 da 28 don cigaba da shari’ar da kuma duba yanke hukunci ga mutanen biyu

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.