• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMNESTY TA BUKACI ‘YAN HOUTHI SU SAKE ‘YAN JARIDA

Kungiyar kare hakkin dan-adam ta AMNESTY ta bukaci ‘yan tawayen houthi su sake ‘yan jaridar Yaman hudu da su ka gabatar gaban kotu har a ka yanke mu su hukuncin kisa.

Wannan kira na zuwa ne gabanin sauraron daukaka karar wannan hukunci mai tsananin gaske biyo bayan samun ‘yan jaridar da laifin cin amanar kasa da zama ‘yan leken asirin kasashen ketare.

Amnesty ta ce ba a yi adalci ba a wajen shari’ar don haka ta bukaci a sake ‘yan jaridar.

Houthi ta kama ‘yan jaridar a babban birnin Yaman San’a’a a shekara ta 2015.

‘Yan jaridar sun hada da Abdul Khaleg Amran, Tawfiq Al-Mansouri, Harith Hamid da Akram Al-Walidi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “AMNESTY TA BUKACI ‘YAN HOUTHI SU SAKE ‘YAN JARIDA”
  1. Thanx for the effort, keep up the good work Great work, I am going to start a small Blog Engine course work using your site I hope you enjoy blogging with the popular BlogEngine.net.Thethoughts you express are really awesome. Hope you will right some more posts.

  2. Great beat ! I would like to apprentice while you amend your site, how could i subscribe for a blog website? The account helped me a acceptable deal. I had been tiny bit acquainted of this your broadcast offered bright clear idea

Leave a Reply

Your email address will not be published.