• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AMA AKANTA-MASU SHARHI NA FATAR EFCC ZA TA KARA DAGEWA

Biyo bayan cafke babban akantan Najeriya Ahmed Idris da zargin wawure naira biliyan 80, masu sharhi na fatar cigaba da daukar matakin ta hanyar ba sani ba sabo ga duk jami’in da a ka samu hannun sa a almundahana.
Masu sharhin na cewa tamkar EFCC ta na barci ne inda har masu ta’annati da dukiya ke ganin ba abun da zai same su.
Ra’ayoyin masu sharhin na nuna ko ba a hukunta masu satar dukiyar jama’a a karkashin wannan gwamnati don wasu dalilai, nan gaba wata gwamnatin za ta bankado bayanan ta hukunta su.
An samu dogon lokaci ba a ji an yi nasarar yanke wata shari’a kan manyan wadanda a ke tuhuma da cin hanci da rashawa ba

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AMA AKANTA-MASU SHARHI NA FATAR EFCC ZA TA KARA DAGEWA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.