• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AL’UMMOMI 42 NA KARKASHIN BARZANAR BOKO HARAM A NEJA-DAN MAJALISAR DATTAWA

Yayin da majalisar dattawan Najeriya ke muhawara kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, dan majalisar dattawa daga Neja Muhammad Sani Musa ya ce yanzu haka kauyuka 42 ke karkashin mamayar boko haram.

Sanata Musa ya ce kimanin mutum 5000 na kauyuka su ka rasa matsugunan su a sanadiyyar shigowar ‘yan boko haram jihar ta arewa ta tsakiyar Najeriya.

Bayanin Sanata Musa na zuwa ne bayan gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya baiyana yanda boko haram ke barazana ga al’ummar jihar.

Sanata Musa ya ce a shekaru bakwai da su ka wuce, ‘yan boko haram sun addabi mazabar dan majalisar dattawa ta Neja ta gabar da kashe-kashe.

Hakan a cewar dan majalisar ya jawo koma baya ga lamuran tattalin arziki da ilimi a yankin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AL’UMMOMI 42 NA KARKASHIN BARZANAR BOKO HARAM A NEJA-DAN MAJALISAR DATTAWA”
  1. You could definitely see your expertise in the article you write.

    The arena hopes for even more passionate writers such as you who aren’t afraid to say how they believe.
    At all times follow your heart.

Leave a Reply

Your email address will not be published.