• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALLAH YA YI WA SHUGABAN DAULAR LARABAWA SHEIKH KHALIFA BIN ZAYED RASUWA

Allah ya yi wa sarkin Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan rasuwa ya na mai shekaru 73 a duniya.

Kanin marigayin Yarima na Abu Dhabi Muhammad Al Nahyan ya ce kasar ta rasa sarki mai nagarta.

Shi ma sarkin Dubai Muhammad bin Rashid Almaktoum ya nuna matukar juyayin mutumin da ya kira jagoran tafiyar su a kasa.

Kasar ta Daular Larabawa ta shiga makoki na tsawon kwana 40 inda kasashen Larabawa da na duniya ke mika sakon ta’aziyyar su.

Khalifa Al Nahyan ya zama shugaba ne a shekara ta 2004 inda ya zama sarkin Abu Dhabi na 16 ya gaji kujerar mahaifin sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ALLAH YA YI WA SHUGABAN DAULAR LARABAWA SHEIKH KHALIFA BIN ZAYED RASUWA”
  1. Good site! I really love how it is easy on my eyes and the data are well written. I’m wondering how I could be notified when a new post has been made. I have subscribed to your feed which must do the trick! Have a nice day!

Leave a Reply

Your email address will not be published.