• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALLAH YA YI WA SHEIKH AHMED LEMU RASUWA

Allah ya yi wa shehun malamin nan kuma tsohon alkali Sheikh Ahmed Lemu rasuwa bayan fama da jinya.

Marigayin ya rasu ya na mai shekaru 91 a duniya. ‘Yar marigayin Maryam Lemu ta baiyana sanarwar daga dan uwan ta Nuruddeen Lemu, cewa Sheikh Lemu ya rasu da sanyan safiyar alhamis a Minna Jihar Neja.

Sheikh Lemu ne ya jagoranci kwamitin duba fitinar da ta biyo bayan zaben 2011 da a ka aiyana tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya lashe yayin da ya yi takara da shugaba mai ci Muhammadu Buhari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *