• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALLAH YA YI WA MATASHIN SOJA MANJO A.D.MUHAMMED RASUWA

Allah ya yi wa matashin soja manjo Auwal Danbabu Muhammed rasuwa a sanadin hatsarin mota a kan hanyar sa daga Gusau zuwa Kano.

Marigayin wanda dan jihar Gombe ya taso ne daga bakin aikin sa daga Zamfara don tafiya gidan sa a Kano daga nan ya zo Gombe murnar idin babbar sallah.

Manjo Muhammed ya rasu a motar da ya ke tukawa tare da matar sa da ‘yar sa mai kimanin shekara biyu.

Manjo Muhammed na daga jami’an soja da ke fafatawa da ‘yan bindiga a dazukan Zamfara.

Ya rasu ya bar mahaifin sa dan kasuwa a Gombe Alhaji Danbubu da sauran ‘yan uwa da su ka hada da Rabi’u Saleh na kamfanin Jewel Times da Imam Mukhtar Abba na babban masallacin Abuja.

Tuni a ka yi jana’izar marigayan a Gusau inda yanzu a ke karbar gaisuwar ta’aziyya a garin Gombe bayan gidan man mega.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *