• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALLAH YA YI WA KWAMANDAN LAMURAN TSARO NA JIWBIS LAWAL SANI RASUWA

Allah ya yi wa kwamandan lamuran tsaro na kungiyar Izala ta kasa Lawal Sani rasuwa a sanadiyyar hatsarin mota.

Marigayi Lawal Sani  mai haba-haba da jama’a da kwazon aiki dare da rana, jami’in sojan Najeriya ne.

Allah ya horewa marigayin kwarewa wajen sana’o’in hannu da su ka kai 200 inda ya kan taimakawa zawarawa da sauran jama’a koyon sana’o’in samun dogaro da kai.

Za a iya kwatanta rayuwar marigayin da wanda ya sadaukar da kan sa ga aiyukan alheri da kwazon ganin jama’a sun samu hanyoyin rayuwa ta hanyar halal.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau na cigaba da karbar gaisuwar ta’aziyyar marigayin ya na mai addu’ar Allah ya jikan sa da rahama ya kuma albarkaci zuri’ar sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *