Rahoton da mu ke samu ya nuna nasarar sako Mallam Mahmud Rufai dan jihar Zamfara wanda masu satar mutane su ka dauke yayin da ya ke tafiyaba daidai garin Sheme a jihar Katsina.
Akalla dai Mahmud ya kai kwana goma a hannun masu satar mutanen.
Wani abun lura shi ne yanda Allah ya hukunta jiragen sama da ke shawagi ba su sako bom kan barayin ba lokacin da su Mahmud ke hannun su.
An yayata sace Mahmud a yanar gizo inda mutane su ka rika addu’ar Allah ya sa ya samu kubuta.
Yanzu haka ‘yan uwa da abokai na tururuwa gidan su Mahmud a Gusau don jajanta lamarin da addu’ar Allah ya kiyaye gaba.
Satar mutane a yankin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja ta zama ruwan dare.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀