Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce Allah ke ba da mulki ga wanda ya so amma zai gwada nema don hakan shi ya fi dacewa.
Osinbajo na magana ne a fadar gwamnatin jihar Ondo a birnin Akure yayin da ya kai ziyara ga gwamna Rotimi Akeredolu.
Yemi Osinbajo ya nuna cewa zai zama an yi asarar basirar da ya tara a tsawon shekaru 7 ya na matsayin mataimakin shugaba matukar bai yi takarar ba.
Ya zaiyana shugaba Buhari a matsayin wanda yak e da budaddiyar zuciya ga kowa kuma ya ba shi damatr gudanar da aiyuka masu muhimmanci.
Za a gudanar da taron fidda gwani na APC a ranar 29 da 30 ga watan nan na mayu zuwa ranar 1 ga watan yuni.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Hello! Would you mind if I share your blog with my myspace group? There’s a lot of people that I think would really appreciate your content. Please let me know. Many thanks