• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALJERIYA TA BA DA LAMUNIN DALA MILIYAN 300 GA TUNUSIYA

ByNoblen

Dec 15, 2021 ,

Kasar Aljeriya ta ba da lamunin dala miliyan 300 ga kasar Tunusiya, kwana daya gabanin ziyarar shugaban Aljeriya Abdelmajid Tebboune.
Sanarwar ta nuna wannan ya biyo bayan amincewar ba da lamunin ne da shugaban Tunusiya Kais Saied ya cimma a ranar 9 ga watan nan.
Tunusiya ta auka matsalar karayar tattalin arziki sanadiyyar cin hanci da rashawa.
Saied ya amshe dukkan madafun ikon kasar ta hanyar fatattakar dukkan jami’ai har ma da dakatar da majalisa don ceto kasar daga kalubale.
Duk da Saied bai baiyana logar da zai bi wajen inganta arzikin kasar ba, ya sanar da za a gudanar da zaben sabuwar gwamnati a shekarar nan ta 2022 mai shigowa

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ALJERIYA TA BA DA LAMUNIN DALA MILIYAN 300 GA TUNUSIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *