• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALHAZAI SUN DAWO MASAUKAN SU A MAKKAH

ByNoblen

Jul 13, 2022

Bayan kammala aikin hajjin bana alhazai daga kasashen duniya sun dawo masaukan su a Makkah don jiran komawa gida.
Yayin da wasu daga alhazan kan huta ko shiga shagunan kayan tsaraba, wajen na leka harabar harami don samun sallah cikin jami’i da kuma samun damar addu’o’i da sauran ibadu.
Kimanin fiye da alhazai dubu 800 ne su ka samu zuwa aikin hajjin a karo na farko da alhazan ketare su ka shigo tun bullar cutar annoba.
Jama’a na fatan hukumomin Saudiyya za su kara bude kofa badi don ninkin alhazan su samu gudanar da wannan Ibada mai muhimmanci sau daya a rayuwar musulmi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ALHAZAI SUN DAWO MASAUKAN SU A MAKKAH”

Leave a Reply

Your email address will not be published.