• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALAMUN JUYIN MULKI-SOJOJI SUN TSARE SHUGABA DA FIRAMINISTA A MALI

A yanzu haka sojoji a kasar Mali sun yi awun gaba da shugaba da firaministan kasar da ke nuna alamu ne na juyin mulki.

Sojojin sun fice da shugaba Bah Daw daga babban birnin kasar Bamako zuwa cibiyar a Kati da ke tazarar kilomita 15 daga bigiren.

Baya ga shugaban, sojojin sun dauke firaminista Moctar Ouane da ministan tsaro Souleyman Doucoure.

Dama sojojin su ka amince nada gwamnatin don aikin maida mulki hannun farar hula bayan sun kifar da gwamnatin shugaba Boubacar Keita a bara.

Masu sharhi na ganin garambawul a gwamnatin da rage yawan sojoji ya sanya daukar matakin mai salon juyin mulki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.