• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ALAMU NA NUNA AN SAMU RABUWAR KAN GWAMNONIN APC GABANIN BABBAN TARO A 26 GA WATAN NAN

ByNoblen

Mar 11, 2022

Alamu na nuna an samu rabuwar kawuna a tsakanin gwamnonin jam’iyayr APC 23 gabanin babban taron jam’iyyar a 26 ga watan nan.
Wannan na zuwa bayan rudanin kwabewa ko akasin haka na gwamna Mai Mala Buni a amtsayin shugaban rikwan jam’iyyar na kara daukar sabon salo.
Zuwa yanzu ba bayani kai tsaye daga shugaba Muhammadu Buhari na nada gwamnan Neja Abubakar Sani Bello a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyyar a babban taro, amma daya daga fitattun gwamnonin APC Nasir Elrufai ya ba da tabbacin shugaba Buhari ne ya kawar da gwamna Buni da hakan ya kawo gwamna Bello kan matsayin.
A zantawa da gidan talabijin na Channels Elrufai ya ce gabanin tafiyar da shugaba Buhari ya yi London don neman magani ya damka alhakin jam’iyayr ga gwamnonin don tabbatar da an gudanar da babban taron kamar yanda a ka tsara.
Elrufai ya ce a bangaren su, su na da gwamnoni 19 cikin 23 da ke bayan gwamna Bello kuma za su tsaya kan sabon shugaban jam’iyyar ya fito daga arewa ta tsakiya duk da bai ambaci sunan Sanata Abdullahi Adamu kamar yanda a ke yayatawa ba, amma ya ce daidaitawa za a yi a fito da sunan mutum daya.
Masana siyasa na cewa duk wannan gwagwarmayar na da alaka da inda ‘yan siyasar su ke son kasancewa a babban zabe mai zuwa.
Sanata Kabiru Gaya bai ture wannan tunanin ba.
Sai dai mai taimakawa gwamna Buni ta lamuarn yanar gizo Haruna Sardauna ya ce sam ba su amince ko gamsu da cewa shugaba Buhari ya ba da wannan umurnin ba.
Yanzu zai yi wuya a dorar da wata magana mai karfi gabanin taron majalisar koli na jam’iyyar da a ke sa ran gabatarwa makwan gobe

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ALAMU NA NUNA AN SAMU RABUWAR KAN GWAMNONIN APC GABANIN BABBAN TARO A 26 GA WATAN NAN”
 1. Greetings! Very useful advice in this particular post!
  It is the little changes which will make the most significant changes.
  Thanks a lot for sharing!

 2. Hey I know this is off topic but I was wondering if you knew of any widgets I could
  add to my blog that automatically tweet my newest twitter updates.
  I’ve been looking for a plug-in like this for quite some time and
  was hoping maybe you would have some experience with something like this.
  Please let me know if you run into anything. I truly enjoy reading your
  blog and I look forward to your new updates.

Leave a Reply

Your email address will not be published.