Sheikh Abubakar Lamido ya nuna matukar takaici ga yanda wasu kan fake da musulunci su rika kisan gilla
A hudubar sa ta sallar jumma’a a masallacin jumma’a na Bolari Gombe, Imam Lamido ya ce sam addinin Islama bai koyar da kashe rai haka kurum ba ta hakkin shari’a ba.
Malamin ya ce addinin musulmi hanya ce ta adalci da rikwan amana ta hanyar tsare dokokin Allah a baiyane da kuma a boye.
Malamin ya yi addu’ar Allah ya shirya duk masu ratse hanya da fakewa da alamun Islama wajen cin zarafi da kashe rayukan da ba su yi laifin komai ba.
Malamin ya bukaci karfafa cusa akida sahihiya ta Islama da ta ce da fahimtar magabata a tafiyar manhajin Ahlussunnah.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀