• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AKWAI RUDANI A HUKUMAR KULA DA RAYA YANKIN NEJA DELTA

Rahotanni na baiyana akwai gagarumar damuwa a hukumar nan ta raya yankin Neja Delta NDDC a takaice.

Bayanai sun nuna binciken da a ke gudanarwa a hukumar ta hanyar kwararrun gano hada-hadar kudi, zai fito da irin babbar badakalar da manyan jami’an hukumar ke da hannu a kai.

Wannan a binciken jaridar THE WILL zai bankado bayanan da a baya ke boye a duhu na almundahana.

In za a tuna tsohon babban daraktan hukumar Farfe Pondei ya suma a gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa.

Duk da makudana kudin da gwamnati ke turawa hukumar, amma ba a ganin wani abun ku zo ku gani da ta ke yi wa mutanen yankin Neja Delta.

Matukar binciken ya tafi a yanda a ka binciko, to za a zubar da jami’an hukumar don nada sabbi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *