• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AKASI-‘YAN SANDA SUN CE RANDAR GAS CE TA FASHE A ANGUWAR SABON GARI A KANO

Binciken da ‘yan sanda ta yi zuwa yanzu kan fashewar wani abu a anguwar Sabon Gari a Kano, na nuna wata randar iskar gas ce ta fashe da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 4.

Wadanda su ka rasu sun hada da maza 3 mace daya inda a cikin su, har da wani mai walda mai suna Ejike.

Wasu na tababar cewa zai yiwu bom ne ya tarwatse ko ma watakila dan kunar bakin wake ne ya tada bom kafin ya isa inda ya nufa.

Rundunar ‘yan sandan dai a Kano ta ba da tabbacin tafiya wajen da dukkan kwararrun binciken bom da sauran makamai masu fashewa inda su ka gano a binciken farko cewa randar iskar gas ce ta kawo hatsarin.

A na hasashen za a iya samun wasu da gini ya danne a bigiren fashewar da ke kan titin Aba a anguwar ta Sabon Gari.

Hukumar agajin gaggawa ta ce za ta fitar da adadin wadanda su ka rasa rai bayan kammala aikin agaji.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
12 thoughts on “AKASI-‘YAN SANDA SUN CE RANDAR GAS CE TA FASHE A ANGUWAR SABON GARI A KANO”
  1. Its like you read my mind! You seem to know so much about this, like you wrote the book in it or something. I think that you could do with a few pics to drive the message home a little bit, but instead of that, this is excellent blog. A fantastic read. I’ll certainly be back.

Leave a Reply

Your email address will not be published.