• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AKALLA MUTUM 7 SU KA MUTU A YUNKURIN SHIGA FILIN TASHIN JIRAGEN SAMA NA KABUL

ByNoblen

Aug 23, 2021 , ,

An kara samun asarar rayuka a filin jiragen sama na Kabul yayin da dafifin ‘yan Afghanistan ke gwagwarmayar shiga filin don ficewa daga kasar.

Rundunar sojan Burtaniya ta baiyana cewa mutum 7 su ka rasa ran su.

Masu gwagwarmayar arcewa daga kasar wadanda su ka yi aiki ne ko hidima ga sojojin Amurka ga na taraiyar turai.

Dakarun Taliban na alwashin ba za su yi ramuwar gaiya ga ma’aikatan turawan ba, amma wasu da dama na cikin firgici da rashin kwanciyar rai.

Filin jirgin na Kabul ne kadai fitacciyar hanyar arcewa daga kasar.

Kungiyar kasashe musulmi OIC ta yi tayin taimkawa wajen kawo zaman lafiya da kwashe masu son hijira daga Kabul.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *