• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AKALLA MUTUM 19 SU KA RASA RAI A YAMAN DUK DA SAMUN ZAMAN TSAGAITA WUTA

Kimanin mutum 19 sun rasa ran su a kasar Yaman duk da aikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta don kawo karshen yakin basasar kasar da ya faro tun 2014.

Cikin wadanda su ka rasa ran su har da yara uku.

Gwamnatin kasar da ke birnin Aden na kudanci ta cimma sabunta tsagaita bude wutar da wata biyu tsakanin ta da ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya.

Jami’ar labaru ta sasahen jinkai na majalisar dinkin duniya Liz Throssell ta ce an samu akasarin asarar rayuka a sanadiyyar fashewar nakiyoyin da a ka bunne.

Throssell ta kara da cewa mutum 32 ne su ka samu raunuka a cikin wata biyu na tsagaita wutar na farko.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AKALLA MUTUM 19 SU KA RASA RAI A YAMAN DUK DA SAMUN ZAMAN TSAGAITA WUTA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.