• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AIYANA BARAYIN DAJI A MATSAYIN ‘YAN TA’ADDA BA ZAI TASIRI BA-DR.AHMAD GUMI

ByNoblen

Nov 29, 2021

Dr.Ahmad Gumi ya ce aiyana barayin daji a matsayin ‘yan ta’adda ba zai yi wani tasiri ba a lamuran tsaro.
Kotu a Abuja ta yanke matsayar aiyana barayin daji a matsayin ‘yan ta’adda biyo bayan bukatar hakan da ta saurarar
Gumi ya ce kamar yanda aiyana ‘yan awaren Biyafars bai yi wani tasiri ba, hakanan aiyana ‘yan bindiga a matsayin masu aikata ta’addanci.
Dr.Gumi na da ra’ayin tattaunawa da barayin shi ne kadai zai iya kawo maslaha a fitinar sace mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun laifuka da a ke fama da su musamman a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Wadanda ba su gamsu da matsayar Dr.Gumi na sukar sa da yunkurin ba da kariya ga barayin da kan cutar da jama’a ba tare sa laifin komai ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AIYANA BARAYIN DAJI A MATSAYIN ‘YAN TA’ADDA BA ZAI TASIRI BA-DR.AHMAD GUMI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.