• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AIKIN HAJJIN BANA-BA ZA A BARI FIYE DA MUTUM 4 SU ZAUNA A DAKI DAYA BA-NAHCON

Shugaban hukumar alhazan Najeriya NAHCON Zikrullah Kunle Hassan ya baiyana cewa a hajjin da a ke shiryawa na bana ba za a bari fiye da mutum 4 su zauna a daki daya ba.
Bayan taruka da masu kula da hidimar alhazan a Saudiyya wato MU’ASSASA, Zikrullah Hassan ya ce kazalika za a hada duk tawagar alhazai 45 da jami’in kula guda daya.
Shugaban na NAHCON ya kara da bukatar duk jami’an alhazan su fara shirin bin wannan ka’ida; kuma hukumar na yin duk abu mai yiwuwa wajen rage tashin kujerar hajjin.
Hakanan shugaban na NAHCON ya bukaci mutane su mika kudin su a kan lokaci don hakan ya ba da damar kammala dukkan tsare-tsare na tafiya hajjn in tafiyar ta taso.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AIKIN HAJJIN BANA-BA ZA A BARI FIYE DA MUTUM 4 SU ZAUNA A DAKI DAYA BA-NAHCON”
  1. I haven’t checked in here for some time since I thought it was getting boring, but the last several posts are great quality so I guess I’ll add you back to my everyday bloglist. You deserve it my friend 🙂

Leave a Reply

Your email address will not be published.