• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AIBANTA MANZO-KOTUN KANO TA DAURE MUBARAK BALA SHEKARU 24

Kaeshe kotu a Kano ta yanke hukuncin daure matashin nan da a ka same shi da laifin aibanta Manzon Allah, Mubarak Bala shekaru 24.
Matashin wanda shi ne shugaban wadanda ba su yarda da Allah ba wato MULHIDAI na Najeriya, ya fada hannun jami’an tsaro ne shekaru biyu da su ka wuce biyo bayan wallafa kalamai na aibanta Annabi Mai tsira da aminci a shafin sa na fesbuk.
Mubarak Bala wanda dan tsohon malamin jamia ne Dr.Bala Muhammad ya ki musanta duk zargi 18 da a ka yi ma sa a gaban kotu.
Matsayar Bala ita ce duk laifin da a ke tuhumar sa da shi ya amince ya aikata kuma bai yi nadama ba.
Bala zai zauna a gidan yari na tsawon shekarun a jere.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AIBANTA MANZO-KOTUN KANO TA DAURE MUBARAK BALA SHEKARU 24”

Leave a Reply

Your email address will not be published.