• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AFGHANISTAN-TALIBAN NA NAUSAWA ZUWA BIRNIN KABUL

ByNoblen

Aug 14, 2021 , , ,

‘Yan Taliban na nausawa don neman kwace babban birnin Afghanistan wato Kabul bayan amshe cibiyoyin larduna 10.

Kama birnin Logar da Taliban ta yi da ke tazarar kilomita 25 daga birnin Kabul ya sanya firgici ga hukumomin na Kabul.

Tuni da ma Taliban ta kwace birni na biyu mafi girma a kasar Kandahar da kuma na uku birnin Herat.

Yanzu haka wasu sojojin gwamnatin Afghanistan sun mika wuya ga ‘yan Taliban inda mutanen sa su ka arce zuwa Kabul ke zaune a tantunan wucin gadi.

Kakakin gwamnatin Kabul Zabibullah Mujahid ya tabbatar da birnin Logar ya fada hannun ‘yan Taliban.

Nasarar gaggawa ta Taliban ta shammaci kasashe inda Amurka da Burtaniyya su ka yi wuf su ka shiga kwashe ‘yan kasashen su daga kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *