• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ADDU’A NA RAGE KAIFIN KORONA BAIROS-DR.AHMED GANA

“..na amince da karfin addu’a ya rage tsanantar korona a Afurka…” Inji kwamishinan lafiya na Gombe Dr.Ahmad Gana. Ya kara da cewa Allah ya kare yankunan Afurka ko Najeriya daga  munin cutar ba kamar yanda a ke hasashe za a yi ta faduwa a kan titi a na mutuwa ba. Likitan ya ce ko a kimiyya akwai addu’a.

Dr.Gana wanda likita ne da ya yi da cibiyoyin lafiya na yammacin duniya ya ce har yanzu cutar ta fi tsanani a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki duk da matakan da su ke dauka na yaki da cutar.

Da wannan likitan ya ce akwai taimakon Allah da ya tausayawa kasashe masu tasowa wajen saukin mutuwa ko yaduwar cutar duk da rashin daukar irin nau’in matakan da kasashe masu karfin ke dauka.

Duk da haka likitan ya ba da shawarar mutane su rika bin shawarar masana kiwon lafiya wajen kaucewa shiga hargitsin jama’a su kuma rika wanke hannu da kaucewa yawan taba hanci musamman in su na kokonton hannun su ya taba waje mai dauke da kwayar cuta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.