Mai sharhi kan lamuran siyasa a Abuja Injiniya Magaji Muhammad Yaya ya ce adalci daga gwamnatocin farar hula ne zai hana sojoji katsalandan a lamuran mulki.
Injiniya Yaya na sharhi ne kan taron kungiyar raya tattalin arzikin Afurka ta yamma ECOWAS kan kasashe 3 da a ka yi wa juyin mulki a yankin da kasa ta 4 Guinea Bissau da shugaban ta Umaro Embalo ya tsallake rjiya da baya duk masu yunkurin sun hallaka da dama daga masu gadin fadar sa.
Yaya ya ce duk wani taro da matakai na ECOWAS ko ma uwar kungiyar Afurka AU ba zai hana wannan bazarana ba, sai in jagoron farar hula sun toshe duk wata kafa da sojoji za su fake da ita wajen amsar madafun iko.
Hakanan mai sharhin ya wanke sojoji daga zargin karbar mulki don son zuciya, duk da ya amince mafi munin mulkin farar hula ya fi mafi ingancin mulkin soja.
ADALCI NE ZAI IYA HANA SOJOJI CIGABA DA JUYIN MULKI A KASASHEN AFURKA-INJINIYA MAGAJI

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀