• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABUJA TA KARA RIKICEWA DA KARANCIN MAN FETUR

Babban birnin Najeriya Abuja ya kara rikicewa da dogayen layukan neman man fetur inda hakan kan sa datse hanyoyi da kawo cikas a zirga-zirga.
Duk da wannan ya fara zama jiki, amma yanda yak an faru a bazata kuma yak wan biyu bai warware bay a sa mutane nuna matukar fushi da korafi.
A wajen birane a kan samu man a gidajen mai amma da farashin da ya sabawa ka’ida, da ya nuna gidajen man sun zama bakar kasuwa.
Direbobin motocin sufuri kan kwana a layin mai kafin su samu shiga ko kuma wasu sai sun mika na goro a bude mu su kofar fita su shiga don shan man.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ABUJA TA KARA RIKICEWA DA KARANCIN MAN FETUR”

Leave a Reply

Your email address will not be published.