• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABUJA TA DAU HARAMAR BABBAN TARON FIDDA GWANI NA JAM’IYYAR APC

Babban birnin taraiyar Najeriya Abuja ya dau haramar babban taron zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki.

Fiye da wakilai 2000 ne za su kada kuri’a in lamarin ya kai ga sai an gudanar da zabe.

Zuwa yanzu akwai ‘yan takara 23 da ke son jam’iyyar ta ba wa daya daga cikin su tikiti don takarar babban zaben 2023 da sauran jam’iyyun hamaiya.

Za a gudanar da taron a dandalin EAGLE da ked aura da fadar gwamnati, majalisar dokokin taraiya da kotun koli.

An dau matakan tsaro saboda taron da a ke sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai halarta tare da gwamnonin jam’iyyar 22.

Masaukan baki sun cika da wakilan da za su yi zaben da sauran mukarrabai inda ‘yan siyasa ke kai kawo don gano alkiblar zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.